Kungiyar ISIS tayi barazanar halaka mutane 2 da take rike da su

Kenji Goto, dake hannun 'yan kungiyar ISIS
Kenji Goto, dake hannun 'yan kungiyar ISIS Reuters

Hukumomin kasar Japan sun yi Allah wadai da barazanar da ‘yan kungiyar IS suka yi, na fille kan wasu mutane 2 da suke garkuwa dasu, in ba a biya musu bukatu ba.‘Yan kungiyar sun yi barazanar hallaka mutanen, ‘yan kasashen Japan da Jordan, in har ba a sako wata mace da ake tsare da ita a gidan yarin Jordan ba. Fraiministan kasar ta Japan Shinzo Abe dake magana cikin fushi, yace ya umarci dukkan ministocin shi suyi aiki don ganin an kwato dan kasar mai suna Kenji Goto.‘Yan kungiyar ta IS suna tsare da Mr. Goto dan kasar Japan da wani matukin jirgin sama dan kasar Jordan, inda suka nemi a sako wata mace ‘yar kunar bakin wake, da ake tsare da ita a gidan yarin kasar Jordan cikin sa’oi 24, ko su hallaka mutanen 2.Tun lokacin da kungiyar ta IS ta fidda hoton Bidiyo, inda ta yi ikrarin hallaka wani dan kasar ta Japan mai suna Haruna Yukawa a karshen mako, hukumomin birnin Tokyo suka fara neman tallafin Jordan don ceto sauran mutumin daya rage a hannun ‘yan ta’addan.A baya ‘yan kungiyar ta IS sun fille kan wasu Amurkawa 2 ‘yan jarida wani Ba Amurken da ‘yan Britaniya 2 masu aiki agaji, kuma sun yi wasu muggan ayyukan, to sai dai kisan Yukawa ne karon farko da suka far wa ‘yan Japan.Yanzu haka ‘yan kungiyar ta IS suna rike da wasu sassan kasashen Iraqi da Syria, inda kasashen duniya ke ci gaba da yunkurin kawar dasu.