Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar dunkin Duniya ta shiga tsakanin Isra’ila da Lebanon

RFI Hausa

Kwamitin tsaro na Majalisar dunkin Duniya ya gudanar da wani taron gaggawa jiya Laraba inda wakilan kwamitin suka tattauna akan yadda za’a kashe Wutar da ke ci yanzu haka tsakanin kasar Lebanon da Isra’ila

Talla

Lura da yadda al’amurra ke dada zafi tsakanin wadannan kassahen 2 wato Isra’ila da Lebanon, ya sa kasar Faransa ta bukaci a gudanar da wannan zaman domin lalabo zaren dumke wannan baraka.

Bayan samun labarin cewar an kashe wasu Sojin Isra’ila 2 da wani dan kasar Spain mai aikin bada agaji na Majalisar dunkin Duniya a wata musayar Wuta da aka yi tsakanin kungiyar Hezbullah ta kasar Lebanon da Isra’ila, mambobin kwamitin su 15 sun hadu domin shiga tsakani.

Wannan sabon tashin hankalin dai ya haifar da fargaba akan yanda za ta kasance tsakanin kassahen da a shekarar 2006 ma said a suka gwabza.

Kwamitin ya ce babbar manufarsa ita ce shiga tsakanin domin kar yakin ya fadada.

An dai fara samun tashin hankalin ne bayan da kasar Isra’ila ta kai hari babu zato babu tsammani a yankin tsaunukan Golan, inda ta kashe wasu jami’an Hizbullah, ciki kuwa, hadda wani Janar din Sojin kasar Iran.

Iran dai ta tabbatarwa Duniya cewar a kwan da sanin cewar Isra’ila fa ta zuba Adashi ne, kuma kul ba dade kul ba jima zata yi kwasa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.