Venezuela

Ana ta kashe jami’an tsaro a kasar Venezuela

Manifestation de l'opposition vénézuélienne à Caracas, le 24 janvier 2015.
Manifestation de l'opposition vénézuélienne à Caracas, le 24 janvier 2015. Reuters/Jorge Silva

Rahotanni daga kasar Venezuela na cewa, kusan kullum sai an kashe jam’in dan’sanda guda, al’amarin dai ya zama ruwan dare. Ya zuwa yanzu dai akalla an kashe ‘yan sanda 268 a cikin shekarar da ta gabata

Talla

Wadannan alkalluma dai na nuna yadda aikin yan’sanda ke fuskantar barazana a wannan kasar, musamman a yayin da suke gudanar da ayyukan su.

Edgar Perez wani dan sanda ne, da ya gamu da ajalinsa a lokacin da wasu ‘yan Bindiga suka bude masa wuta a hanyarsa ta komawa Gida

Wannan lamari ko a cikin Watan Nuwamban Baara , sai da wasu ‘yan Bindiga suka harbe wasu ‘yan sanda 5, wanda ya kawo adaddin mutane 268 da suka mutu cikin shekarar ta 2014 a kasar ta venezuella.

Masu sa Ido a kasar dai na cewa yawanci ‘yan sandan, ana kai masu hari ne a cikin Motoci, da Babura, ko wurin buga Waya.

Majalisar dinki Duniya dai na cewa lura da yadda ake yawaita samun ‘yan daba a sassa daban-daban na kasar, da kashe ‘yan sanda da lawyoyi ba tare da daukar matakai ba kuma hakan, ya nuna cewa kasa ce da ta fi kowace kasa a Duniya, samun yawan kisan kai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.