Isa ga babban shafi
Lebanon-Faransa

Lebanon za ta fara karbar makamai daga Faransa

Firaministan Lebanon Tammam Salam
Firaministan Lebanon Tammam Salam Reuters/Jamal Saidi
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 1

Faransa ta ce kasar Lebanon za ta fara karbar makaman da Saudiya ta biya daga hannunta a watan Afrilu mai zuwa don yaki da mayakan kasar da ke da’awar Jihadi. Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ne ya tabbatar da haka a lokacin da ya ke ganawa da Firaminsitan Lebanon Tammam Salam a birnin Munich na Jamus.

Talla

Saudiya ce dai ta yi alkawalin biyan kudin makaman daga Faransa da suka hada da makaman Atilare da kuramen jirage yaki da masu liken asiri da kuma motocin yaki masu sulke.

Shugabannin kasashen biyu sun yi kira ga kungiyar Tarayyar Turai ta kawo wa Lebenon dauki wacce ke hidima da miliyoyan ‘yan gudun hijirar Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.