Isa ga babban shafi
UNESCO

Ana bikin ranar Rediyo a duniya

UNESCO
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
1 min

Yau ranar 13 ga watan Fabrairu Hukumar UNESCO ta ware a matsayin ranar Rediyo ta duniya. Kuma bikin na yau wanda shi ne karo na hudu ya mayar da hankali akan kira a ba matasa dama ‘yan kasa da 30 a aikin yada labarai a duniya.

Talla

Wannan rana ce da ake nuna yadda Rediyo ke shafar rayuwar bil’adama, da kuma kusantar da jama’a a ga juna a sassan duniya.

Hukumar ci gaban ilimi da kimiya da al’adu ta UNESCO ta ware ranar ne domin fadakar da al’umma game da muhimmacin Rediyo tare da inganta aikin yada labarai a Rediyo.

A bara ranar ta mayar da hankali ne wajen kira ga kafafen Rediyo su dama da Mata ga aikin yada labarai.

A bana kuma ranar ta mayar da hankali ne wajen kira a ba matasa ‘yan kasa da shekaru 30 maza da mata dama ga aikin yada labarai.

A cikin sakonta shugabar UNESCO Irina Bokova ta bayyana yadda ake samun karancin Matasa ga aikin yada labarai.

Bokova ta ce Rediyo hanya ce da ke ba matasa damar bayyana matsalolinsu da hanyoyin ci gaban rayuwarsu.

Ta ce Matasa ne ke iya gudanar da aikin Jarida a wurare mafi hatsari, don haka akwai bukatar a kara ba su kwarin guiwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.