WHO

Syria: WHO ta nemi karin tallafi

Sansanin 'Yan gudun hijira na Mutane Sudan ta Kudu kusan 17,000 da uska gujewa gidajensu
Sansanin 'Yan gudun hijira na Mutane Sudan ta Kudu kusan 17,000 da uska gujewa gidajensu Reuters/Andreea Campeanu

Hukumar lafiya ta WHO ta bukaci kasashen duniya su kara tallafa wa da kimanin dalar Amurka biliyan daya, domin gudanar da ayukan jinkai a wasu kasashe 4 da ke bukatar agajin gaggawa, kasashen sun hada da Syria da Jamhuriyar Afrika ta tsakiya da Iraki da kuma kasar Sudan ta kudu.

Talla

A taron da kasashen 50 suka Gudanar a birnin Geneva karkashin jagoranci Majalisar Dinkin Duniya hukumar ta bukaci tallafin don taimakawa miliyoyin al’ummar kasashe hudu da yaki ya jefa rayuwar su cikin wani hali, musamma a fanin lafiya.

Hukumar ta bayyana cewa tana bukatar wanna tallafin cikin gaggawa don warkar da akalla mutane miliyan 21 da ke fama da munana raunika da cututuka, da kuma samar da rigakafi da magunguna na kanana yara dake fama da cututuka da dama.

Kusan rabin wanna talafi da hukumar ke nema ta ce za ta yi amfani da su ne a kasar Syria, wanda a yanzu aka shafe sama da shekaru hudu ana yaki, sai kasar Iraqi wace ke bukatar sama da dala miliyan biyu don samar da lafiya ga wasu ‘yan kasar miliyan hudu.

Hukumar kuma ta kara da cewa kasar sudan ta kudu na bukatar dala miliyan 90 don bada magani ga wasu mutane kusan miliyan uku da rabi.

Yayyin da afrika ta tsakiya ke bukatar dala miliyan 48 don taimakawa mutane kusan miliyan guda da rabi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.