Rasha

Za a binne shugaban adawar Rasha da aka kashe

Dubban mutanen Rasha da ke jimamin kisan shugaban adawa Boris Nemtsov,
Dubban mutanen Rasha da ke jimamin kisan shugaban adawa Boris Nemtsov, REUTERS

Dubban mutanen Rasha da ke jimamin kisan shugaban adawa Boris Nemtsov, sun hada gangami a Moscow domin bikin Jana’izarsa a yau Talata. Gwamnatin Rasha ta haramta wa shugabannin adawa halartar taron Jana’izar.

Talla

A ranar Juma’a ne aka bindige Boris Nemtsov babban mai adawa da shugaba Vladimir Putin, lamarin day a girgiza al’ummar Rasha.

Idan an jima ne za a binne shi a makabartar birnin Moscow Troyekuroyskoye.

Amurka da Kasashen yammaci da dama sun yi allawaddai da kisan shugaban adawar.

Tuni dai gwamnatin Rasha ta musanta zargin da ‘Yan adawa ke yi akan tana da hannu ga kisan Nemtsov

Amma zuwa yanzu babu wani da gwamnatin kasar ta cafke wanda ake zargi da kisan shugaban na ‘Yan adawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.