Najeriya

Shugabannin duniya sun taya Buhari murna

Janar Muhammadu Buhari
Janar Muhammadu Buhari AFP PHOTO /STRINGER

Shugabanin Kasashen duniya sun taya Janar Muhammadu Buhari murnar lashe zaben shugabancin Najeriya da aka gudanar a karshen makon da ya gabata. Shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya jinjinawa shugaban Najeriya mai barin gado Goodluck Jonathan kan rawar da ya taka a zaben, tare da taya Janar Buhari murna da kuma shirin aiki tare da shi. 

Talla

Philips Hammond, sakataren harkokin wajen Birtaniya, ya taya Buhari murnar zama shugaban Kasa, kuma a cewarsa Birtaniya na da kyakkyawar alaka da Najeriya, lamarin da ya sa Hammond ya yi burin cewa, za su yi aiki tare da sabon shugaban Kasar.

Kasar Faransa ta bayyana farin cikinta ga daukacin al’ummar Najeriya kan wannan nasara inda tace shugaba Francois Hollande zai tattauna ta waya da zababben shugaban kasar Janar Muhamamdu Buhari, kana kumazata tura ministan harkokin wajen ta Laurent Fabius halartar rantsar da shi.

Kazalika Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, ya yi wa Buhari barkan lashe zabe, kuma ya kara da cewa ya yi magana da Buhari da Jonathan dangane da sakamakon da hukumar INEC ta fitar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.