WHO
Kula da tsabtar abinci na yin kariya ga lafiya
Wallafawa ranar:
Yau 7 ga watan Afrilu Majalisar Dinkin duniya ta ware a matsayin ranar kiwon lafiya ta duniya. Kuma bikin na bana ya mayar da hankali wajen wayar da kan al’umma game da muhimmacin kula da tsabtar abinci.
Talla
Alkalumman hukumar lafiya ta duniya WHO sun nuna cewa rashin kula da tsabtar abinci na haifar da cututtuka da dama.
Rahoton hukumar ya ce rashin kula da tsabtar abinci na haifar da Cututtuka sama da 200. Kuma an kiyasta cewa kimanin mutane miliyan 2 ke mutuwa duk shekara saboda rashin samun abinci da ruwan sha masu tsabta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu