Jirgin ruwa ya nutse da bakin haure 400 a teku
Wallafawa ranar:
Rahotanni daga kasar Italia sun ce akalla bakin haure 400 ake sa ran sun mutu lokacin da kwale kwalen da suke ciki ya kife akan hanyarsu ta zuwa Turai daga Libya. Jami’an kula da gabar ruwan Italia sun ce sun ceto 144 daga cikin bakin hauren da suka nitse, tare da gawarwaki 9.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira da kungiyar agaji ta Saves the Children sun ce tsakanin baki 144 zuwa 150 suka yi sa’ar isa bakin gabar ruwan Reggio Calabria da ke Italia yau Talata.
Kungiyar Tarayyar Turai ta ce daga ranar Juma’ar da ta gabata an yi nasarar ceto kimanin bakin haure 7, 000.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu