Saudiyya Za Ta Baiwa Yemen Dollan Amirka miliyan 274
Wallafawa ranar:
Kasar Saudiyya wadda take jagorantar hare-hare kan ‘yan tawayen Yemen na tsawon makonni uku yanzu, ta yi alkawarin bada agajin kudin Amirka Dolla miliyan 274 don gyara kasar Yemen.Yau asabar Saudiyya ta bayyana wannan taimako.Bayanai na cewa Sarki Salman na Saudiyya ya bada umarnin kai agajin, bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta nemi a taimaka domin tallafawa dimbin mabukata agaji a kasar ta Yemen.