WHO

Daya daga cikin yara Biyar basa samun rigakafi-WHO

Yara
Yara

Hukumar lafiya ta Duniya WHO tace har yanzu akwai yara kanana da dama, da ba a musu allurar riga kafi ba a fadin duniya.

Talla

Shugaban sashin kulla da rigakafi na Hukumar Jean-Marie Okwo-Bele ta ce kowanne daya cikin 5 na yara basa samu ana musu alluran, da ke kare yara daga kamuwa da cutuka da ke jefa rayuwar su a ciki hadari.

Jean-Marie ta ce kimani yara miliyon 22, wanda akasarin su daga kasashe ‘yan rabbana ka wadata mu, basu samu an musu allurar ba a sheakarar 2013.

Mafi yawa daga cikin wadanan yara sun hadda da ‘yan kasar India da Pakistan da Najeriya kamar yadda Hukumar WHO ta sanar, inda ta bukaci haddin kan al’ummah domin ceto rayukan yaran wadanda rashin rigakafin ke nakasarwa ko Ajalinsu

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI