Isa ga babban shafi
Duniya

Bankin Duniya ya ce Canjin yanayi na barazana ga cigaba

Mutane na gangami dangane da sauyin yanayi a birnin New York
Mutane na gangami dangane da sauyin yanayi a birnin New York Reuters/Eduardo Munoz
Zubin rubutu: Umaymah Sani Abdulmumin
1 min

Bankin duniya yace canjin yanayi na haifar da babbar barazana ga ci gaba, kuma dole ne kasashen duniya su yi kokarin kowa karshen matsalar.

Talla

Shugaban bankin na duniya Jim Yong Kim yayi gargadin cewa dole gwamnatoci su gaggauta daukar matakai, don takaita matslara dumamar yanayi, da kula da tsare tsaren da za su samar da ci gaba mai dorewa, don kaucewa shiga matala.

Kim dake magana yau Alhamis a taro kan muhalli a da aka yi a birini Hong Kong, yace kamata yayi kasashen duniya su yi wani abu kan lamarin acikin wannan shekarar.

Sai dai kuma Jagoran yankin  Hong Kong Leung Chin-ying  ya ce fadin matsalolin abin sauki ne, akan fadin hanyoyin kawo karshan matsalar, dan haka awaki bukatar samun gudumawa kowani mutum domin shawo kan matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.