G7-Najeriya

Kungiyar G7 za ta taimaka wa Najeriya

Sakataren Harakokin Wajen Amurka john Kerry yana ganawa da Janar Muhammadu Buhari Dan takarar Shugaban kasa a Jam'iyyar adawa ta APC
Sakataren Harakokin Wajen Amurka john Kerry yana ganawa da Janar Muhammadu Buhari Dan takarar Shugaban kasa a Jam'iyyar adawa ta APC Reuters

Kungiyar Kasahse 7 ma su karfin karfin tattalin arzikin masana’antu a duniya sun sha alawashin taimakawa Najeriya shawo kan matsalolin ta. Jakadan kasar Jamus a Najeriya Michael Zenner ne ya bayyana haka yayin da ya ke mikawa Janar Muhammadu Buhari takardar gayyatar halartar taron kungiyar da za a gudanar a a Jamus makon gobe.

Talla

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ce ta aiko wa Buhari da goron gayyata.

Kungiyar ta kun shi kasahsen Amurka da Jamus da Birtaniya da Italya da Japan da Canada.

Jakadan Faransa a Najeriya Denys Gauer ya mikawa Janar Buhari takardar gayyata daga shugaba Francois Hollande da kuma alkawarin taimakawa kasar magance matsalar Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI