Faransa

Faransa ta yi gargadi akan sauyin Yanayi

Laurent Fabius minista harkokin wajen Faransa
Laurent Fabius minista harkokin wajen Faransa AFP PHOTO / KENZO TRIBOUILLARD

Hukumomin Faransa sun yi gargadin cewa kasashen duniya ba su da zabi, face su tunkari matsalar canjin yanayi ka’in da na’in, don wannan duniyar kawai ake da ita.Ministan harkokin waje Laurent Fabius da ke jawabi wajen bude taron kwanaki 2, akan yanayi a birnin Berlin na kasar Jamus, ya ce dole ayi aiki ba kama hannun yaro, don ganin an sami nasara kan lamarin.

Talla

Taron da kasashe 35 ke halarta zai samar da hanyoyin da za'a rage gurbatacciyar iskar da ake fitarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.