Mutane 42 sun mutu a rikici 'yan sanda da masu fataucin kwayoyi a Mexico
Wallafawa ranar:
A kalla mutane 42 ne suka rasa ransu a kasar Mexico, lokacin da aka yi musayar wuta tsakanin ‘Yan Sanda da wasu da ake zargi gungun masu fataucin kwayoyi ne. Hukumomin kasar sun ce wani dan Sanda 1 ma ya rasa ranshi a rikicin, da aka yi a garin Tanhuato, dake jihar Michoacan, lokacin da jami’an tsaron suka tsare wata mota da ake zargin tana dauke da kwayoyi, inda mutanen ciki suka bude wuta.Harbin da mutanen suka yi ya sa ‘yan sanda suka mayar da martini, inda aka raraki wadanda ake zargin har zuwa cikin daji.Wannan na daya daga cikin rikici mafi muni, a kokarin da hukumonin kasar keyi na yaki da gungiyoyin da ke hada hadar kwayoyi.