Bukatar kasashen kudanci Amurka zuwa Nicolas Maduro
Wallafawa ranar:
Tsoffin Shugabanin Spain da yankin kudancin Amurka 27 sun bukaci shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro da ya saki firsinonin siyasar da ya daure ya kuma kare hakin Bil Adama a cikin kasar.
Sanarwar na zuwa ne bayan tsoffin shugabanin kasar guda biyu sun kasa samun damar ganawa da wasu yan adawa da ake tsare da su Leopold Lopez da Daniel Ceballos.
Shugabanin sun bukaci gwamnatin kasar da ta samar da yanayi mai kyau da zai haifar da tattaunawar siyasa.
Cikin shugabanin sun hada da Alvaro Uribe, Felipe Calderon, Belisario Betancur da Andres Pastarana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu