Britaniya

Bukatar ficewar Britaniya daga Turai ya tsallake mataki na farko.

Firiya minista Britaniya, David Cameron.
Firiya minista Britaniya, David Cameron. AFP PHOTO / THIERRY CHARLIER

Bukatar Birtaniya na ficewa daga kungiyar kasashen Turai ya tsallake matakin farko a Majalisar kasar, sai dai matakin ya dada fito da bambancin da ke tsakanin 'yayan Jam’iyyar Firiya Minista David Cameron.

Talla

Majalisar kasar ta bayyana goyan bayan ta ga kungiyar kasahsen Turai da kuri’u 544 yayin da 53 suka ki amincewa da ita, sai dai Firiya Minsitan na bukatar ganin an baiwa al’ummar kasar damar bayyana ra’ayin su ta hanyar kuri’ar Jin ra’ayin Jama’a.

Sakataren harkokin wajen kasar Philip Hammond ya ce lokaci ya yi da za’a nunawa kungiyar EU cewar Jama’a take yiwa aiki, ba zaman kanta take ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.