Amurka

An Kashe 'Dan Bindiga da ya Kai Hari Ofishin 'Yan Sanda a Dallas na Amirka

Harabar ofishin 'yan sanda a Dallas da aka yi ruwan wuta
Harabar ofishin 'yan sanda a Dallas da aka yi ruwan wuta REUTERS/Rex Curry

Jamian tsaro a kasar Amirka sun gaskata cewa mutumin da akayi artabu dashi tsawo dare a lokacin da yayi ta ruwan wuta a headkwatan ‘yan Sanda dake Dallas yam utu. 

Talla

Bayanan na cewa mutumin ya mutu ne bayan da gwanayen harbi na musamman da ake dasu suka aunashi a cikin motar da yake boye suka dirka masa bindiga.

Mutumin ance ya dasa bama-bamai a harabar ofishin ‘yan sandan sannan yayi ta ruwan wuta cikin dare lokacin da ya kutsa kai cikin mota.

Wani da aka ce mahaifin mutumin ne, Jimmy Lee Boulware  mai shekaru 73 ya kai kansa wajen ‘yan Sanda kuma ya shaida masu cewa dan nasa ya hasala ne da ‘yan sanda  saboda rawar da suka taka a rikicin samun halaccin wani da da aka Haifa masa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.