Amurka ta soki Masar akan Morsi
Wallafawa ranar:
Fadar White House a Amurka ta bayyana damuwa akan hukucin kisa da aka yanke wa Tsohon shugaban Masar Mohammed Morsi. Amurka ta danganta hukuncin da Siyasa, yayin da kungiyoyin kare hakkin Bil’adama ke nuna adawa da yadda mahukuntan Masar ke karya ‘yan rajin kare hakkin bil’adama a kullum.
Amurka tace siyasa ce ta yi tasiri ga hukuncin kisa da Kotun Masar ta yanke wa Mohammed Morsi zababben shugaban kasa na farko a kasar.
Amurka dai ta bayyana damuwarta akan hukuncin. Kuma wannan na iya shafar huldar da ke tsakanin kasashen biyu.
Wannan na zuwa ne kuma a yayin gungun kungiyoyin kare hakkin Bila’adama a Masar ke bayyana adawa da yadda mahukuntan kasar ke murkushe ‘yan rajin kare hakkin bil’adama da kungiyoyin fararen hula.
Tun lokacin da Sojoji suka hambarar da gwamnatin Morsi a 2013, mahukuntan Masar ke kamewa tare zartar da hukuncin kisa akan magoya bayan Jam’iyyar ‘yan uwa Musulmi.
HRW da Amnesty na daga cikin kungiyoyin da suka soki gwamnatin Masar da murkushe ‘yan adawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu