Masar-Isra'ila

Masar ta aika da jakada zuwa Isra'ila

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al Sissi
Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al Sissi REUTERS/The Egyptian Presidency/Handout via Reuters.

Gwamantin Masar ta nada sabon jakada zuwa Isra’ila, bayan da tsohuwar gwamnatin kasar ta Muhammad Morsi ta janye dama rufe ofishin jakadanci kasar  a shekara ta 2012.

Talla

Kamfanin dillancin labaran kasar MENA, ya ce an nada Hazem Khairat tsohon jakadan kasar a Chile a matsayin sabon manzon kasar a Tal Aviv, nadin da tuni Firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu ya bayyana farin cikinsa a kai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI