Amurka-Faransa

Amurka ta nadi zantukan shugabannin Faransa-Wikileaks

Shugabannin Faransa Jacques Chirac da Nicolas Sarkozy da François Hollande
Shugabannin Faransa Jacques Chirac da Nicolas Sarkozy da François Hollande DSK / AFP

Gwamnatin Faransa ta ce ba za ta lamunce wa Amurka ba tana ma ta leken asiri, bayan shafin tonon silili na Wikileaks ya kwarmato cewa Amurka ta dade tana nadar zantukan shugabannin Faransa tun zamanin Jacques Chirac.

Talla

Jaridun Faransa sun ruwaito Wikileaks na cewa Amurka ta nadi zantukan tsoffin shugabannin kasar guda biyu Jacques Chirac da Nicolas Sarkozy, da kuma shugaba mai ci na yanzu Francois Hollande.

Faransa ta ce ba zata amince ba musamman aminiyarta na leken asirinta.

Yanzu haka shugaba Hollande ya kira taron gaggawa tsakanin shi da shugabannin tsaron Faransa domin tattauna rahoton leken asirin.

Amurka ta ki cewa komi kan zargin da ake ma ta.

Ko da ya ke Mai Magana da yawun Majalisar Tsaron Amurka Ned Price, ya ce ba a nadi zantukan Hollande ba.

A cewar Price, Faransa da Amurka na aiki tare kan manufofin kasashen duniya, tare da danganta kasashen biyu a matsayin aminan juna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.