Isa ga babban shafi
Faransa-Burkina

Faransa ta dakatar da Sojojinta 2 kan zargin lalata da yara

Ministan tsaron Faransa  Jean Yves le Drian
Ministan tsaron Faransa Jean Yves le Drian RTL

Ma’aikatar Tsaron Faransa ta sanar da korar sojojinta guda biyu da ake zargin sun yi lalata da kananan yara a kasar Burkina Faso. Ministan tsaron kasar Jean Yves le Drian ya bukaci ma’aikatar shari’ar kasar ta kaddamar da bincike bayan an gabatar ma sa da rahotan zargin.

Talla

A can baya gwamnatin Faransa ta kaddamar da irin wannan bincike kan sojojin kasar da aka zarga da irin wanan laifi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Daya daga cikin yaran da Sojojin suka yi lalata da su akwai ‘yar shekaru biyar wacce mahaifinta ya tsinci hotunan da ke nuna yadda aka ci zarafin ‘yarsa.

Nan take ne Mahaifin ya ruga zuwa ofishin jekadancin Faransa a Ouagadougou tare da sanar da ‘Yan Sanda da ke kan bincike akan zargin.

A yau Laraba ne Jami’an Faransa da ke gudanar da bincike akan zargin lalata da ake wa Sojojin kasar za su isa Burkina Faso daga Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.