Najeriya ta mayar wa wani Bafaranshe kudadensa da aka damfara
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Hukumar EFCC da ke yaki da tu'amulli da kudaden jama'a a Najeriya ta mayar wa wani Bafaranshe da kudadensa yuro 10,000 da wani ya yi amfani da suna da hoton Mace ya damfare shi a Intanet da nufin za ta same shi Faransa su yi aure.
Hukumar EFCC ta ce Bafaranshen mai suna Francois Mercade, ya hadu da Matar ne kyakkyawa mai suna Kate Williams a Intanet a 2009, daga nan ne suka fara soyayya har ta kai su ga batun aure.
Bayan Mercade ya nemi Williams ta same shi a Faransa ne ta bukaci kudi a wajen shi domin kalubalantar wani Kamfani da ta yi wa aiki wanda ya ki biyanta hakkinta. Sannan za ta yi amfani da sauran kudaden ta same shi a Faransa.
Nan take ne Bafaranshen ya turawa Matar kudi yuro 25,000 domin ta biya bukatunta kuma ta same shi a Faransa, kafin ya fahimci ashe damfarar shi aka yi.
Hukumar EFCC ta ce Namiji ne ya damfari Bafaranshen mai suna Omodara Adedapo Oluseye, dalibin wata babbar kwaleji a kudancin Najeriya.
EFCC kuma ta yi kokarin kwato yuro 10,000 daga cikin kudaden da aka damfari Bafaranshen.
‘Yan damfara a Intanet dai sun yi yawa a Najeriya, inda suke amfani da sunan mata da hoto domin damfarar mutane.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu