Rasha

Za a fara taron kasashen BRICS a Rasha

Shugabannin Kasashen Brics
Shugabannin Kasashen Brics REUTERS/Sergei Karpukhin

A gobe Alhamis ne za a bude babban taron kasashen BRICS a birni Oufa dake Rasha, kuma taron zai maida hankali ne kan irin rawar da Rasha ke takawa a Duniya a fannonin da suka shafi tattalin arziki da makamanci sa. 

Talla

Shugabanin kasashen Afrika ta kudu, India, China da Brazil na daga cikin mutanen da za su halarci wannan taron.

Ana sa ran Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya gana da takwaransa na China Xi Jinping yayin da Firai Ministan India Narendra Mohdi  zai halarci Rasha a jajuburin ranar baban taron kasashen dake karkashin inuwar kungiyar Brics.

Shugabanin wadannan kasashe za su tattauna ne kan batutuwa da suka shafi tattalin arziki tare da nunawa duniya cewa kasar Rasha na daya daga cikin kasashe a duniya da ake damawa da ita.

Hukumomin Rasha dai na ci gaba da kokari domin samun goyan bayan kasashe kamar su Brazil, India, China dama Afrika ta kudu.

Fadar shugaban kasar Rasha ta bayyana shugaban Iran a matsayi babban bako a wanan gangami, inda ake sa ran Hassan Rouhani Shugaban na Iran zai gana da Vladmir Putin na Rasha.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI