Vatican

Fafaroma ya kammala ziyara a Kudancin Amurka

Ziyarar Fafaroma Francis a kasashen Kudancin Amurka
Ziyarar Fafaroma Francis a kasashen Kudancin Amurka REUTERS/Osservatore Romano

Fafaroma Francis ya kammala ziyarar kasashen da ke kudancin Amurka inda ya samu tarbar dubban mutane a kasashen Ecuador da Bolivia da Paraguay. Fafaroma ya yi kira akan yaki da talauci da daidaito da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Talla

Ziyarar da ya kai unguwar marasa galihu a Paraguay ya dada nuna goyan bayan da ya ke yi wa al’ummomin da ba su da karfi a kasar da ke da mutane miliyan 7 amma kuma kashi 40 daga cikin su duk matalauta ne.

A ranar Lahadi ne Fafaroma ya koma fadarsa ta Vatican, kuma rahotanni sun ce zai sake kai ziyara kasashen Latin Amurka a watan Satumba, a lokacin da zai kai ziyarci Cuba da Amurka da suka sasanta da juna bayan shafe shekaru 50 suna takun-saka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI