IRAN-Nukiliyya

An cim ma yarjejeniyar shirin Nukiliyar Iran a Vienna

Ministan harkokin wajen Iran  Javad Zarif, à Vienne
Ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif, à Vienne REUTERS/Leonhard Foeger

Manya kasashen duniya da ke tattauna batun shirin Nukiliyar Iran sun cim ma matsaya a yau talata, bayan kwashe tsawon daran jiya suna tattaunawa.

Talla

Kasashen da suka hada da Amurka da Russia da China da Britaniya sai Faransa da Jamus da kuma Iran sun shafe sama da mako biyu suna  kokarin kai ga wannan gaba a Vienna.

Ana dai saran yarjejeniya zai baiwa Iran daman aiwatar da shirin samar da shirin ta na Nukiliya amma da sa ido majalisar dinkin duniya domin tabbatar da cewar ba ta kaucewa sharudan da aka gindaya ma ta ba.

Kana za a cire mata takunkumi da kasashen yammaci da ma Majalisar dinkin duniya suka kakaba ma ta na hana siyar wa kasar da makamai.

Cim ma wannan matsaya na kara nuna irin rawar ganin da Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya yi tun bayan hawan sa Mulki a cikin shekarar ta 2013.

Sama da shekaru 13 kenan da Iran ke kokarin samun wannan daman, sai dai a baya kasashen duniya sun ki amincewa da Iran cewa shirin Nukiliyar ta na zaman lafiya ne.

Yarjejeniyar dai a yanzu zai kasance babban ci gaba da gwamnatin Rouhani.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.