EU-IRAN

Tarrayar Turai ta tsawaita takunkumin da ta kakabawa Iran

Taron tattauna batun Nukiliyar Iran da manyan kasashen Duniya
Taron tattauna batun Nukiliyar Iran da manyan kasashen Duniya REUTERS/Denis Balibouse

Kungiyar Kasashen Turai ta sanar da tsawaita takunkumi da ta kakabawa kasar Iran na watanni shida nan gaba wanda zai kare aiki a watan Janairu na shekara mai zuwa.

Talla

Sanarwar da kungiyar ta bayar bayan kulla yarjejeniyar nukiliyar Iran, kungiyar kasashen Turai tace takunkumin da ta sanyawa Iran zai ci gaba da aiki na watanni shida masu zuwa har zuwa 14 ga watan Janairu na shekara mai zuwa.

Sanarwar ta ce matakin zai baiwa kungiyar damar daukan matakan da suka dace wajen aiwatar da shirin hadin kai na yarjejeniyar da Iran ta kulla da kasashen duniya.

Sau da dama kungiyar ta Turai tayi ta tsawaita takunkumin dan bada damar cimma matsaya tsakanin Iran da wakilan kasashen Birtaniya, Faransa, Amurka, Jamus, Russia, Chana da kuma ita kungiyar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.