IRAN-Birtaniya

Birtaniya za ta bude Ofishin jakadancinta a Iran

Zauren tattaunawa tsakanin Manyan kasashen duniya da Iran kan batun nukiliya
Zauren tattaunawa tsakanin Manyan kasashen duniya da Iran kan batun nukiliya REUTERS/Leonhard Foeger

Kwana daya bayan cimma yarjejeniya tsakanin Iran da Manyan kasashen duniya shida, kasar Britaniya ta sanar da shirin ta na sake bude ofishin jakadancinta dake Tehran babban birnin Iran.

Talla

Sakataren harkokin wajen kasar ta Brittaniya Philip Hammond ne  ya sanar da haka a yau laraba cewar Britaniya na fatan ganin ta bude ofishin jakadancinta dake Tehran kafin karshen wannan shekarar, ya kuma ce bude ofishin zai biyo bayan warware wasu batutuwa da bai yi Karin haske a kai ba.

Tun a shekara ta 2011 kasar Britaniya ta rufe ofishin nata bayan tabarbarewar dangataka tsakanin kasashen biyu.

Hakazalika kasar Iraki dake makwabtaka da Iran da a yanzu tattalin arzikinta ya dogara kan man fetur, ta bayyana farin ciki dangane da cimma yarjejeniyar Nukiliyar Iran ganin hakan zai kawo daidaito da bunkasa a hadadar kasuwanci a yankin, musamman ganin yadda Iraki ke kokarin cike gibi sakamakon hasarar data tafka sanadiyar karyewar farashin mai a kasuwanin duniya.

Duk wannan ya biyo bayan cimma matsaya da Iran da Manyan kasashen duniya da suka hada da Amurka, da China da Britaniya da Faransa da Jamus suka yi ne a Vienna babban birnin Austria.

Yarjejeniya da za ta baiwa Iran damar aiwatar da shirinta na Nukiliya amma fa, da sa idon majalisar dinkin duniya domin tabbatar cewar ba ta kauce wa sharuddan da aka gindaya ma ta ba, yayin da za a cire ma ta takunkumin da kasashen yammaci da ma Majalisar dinkin duniya suka kakaba ma ta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI