Turkmenistan

Turkmenistan tafi kowacce kasa karancin mashaya sigari

A man smokes an e-cigarette
A man smokes an e-cigarette AFP PHOTO/Nicoals Tucat

Hukumar lafiya ta Duniya WHO tace kasar Turkministan ce tafi kowacce karancin mashaya taba sigari a fadin duniya.

Talla

Shugabar hukumar ta WHO Margaret Chan ce ta fadi hakan, a lokacin wata ziyarar da ta kai a kasar, dake karkashin tsohuwar Tarayyar Soviet.

Chan ta shaida wa shugaban kasar ta Turkmenistan Gurbanguly Berdymukhamedov, da shima likitan hakora ne, cewa alkaluman da hukumar ta WHO ke dasu, sun nuna cewa kashi 8 cikin 100 na ‘yan kasar ne kawai suka taba zukar taba sigari.

Tabar sigari dai na tattare da illoli masu barazana ga lafiyar mai shanta cikin illolin akwai matsalar huhu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI