Libya

Turai da MDD sun soki hukuncin da aka yanke wa Seif Islam a Libya

Seif al-Islam Gadafi
Seif al-Islam Gadafi REUTERS/Stringer/Files.

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Tarayyar Turai, sun yi kakkausar suka dangane da hukuncin kisa da kotu ta yanke wa dan tsohon shugaban Libya Seifil Islam Kaddafi da wasu mutane 8 bayan samunsu da hannu wajen azabtar da jama’a da kuma kisa, a lokacin da jama’a ke boren nuna adawa da gwamnatin mahaifinsa shekaru 47 da suka gabata.

Talla

Da farko dai Kotun duniya ta bukaci a mika ma ta Seifil Islam domin hukuntar da shi, abin da hukumomin kasar Libya suka ki amincewa da shi.

Kotun Libya kuma ta yanke hukuncin ne ba a idon Seif Islam ba wanda yanzu haka ke hannun mayakan da ke jagorantar gwamnati a Zintan wadanda ke adawa da mahukuntan Tripoli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.