Isa ga babban shafi
FIFA

An nuna ba a son Blatter a fadin duniya- Yarima Ali

Yariman Jordan Ali Bin Al Hussein
Yariman Jordan Ali Bin Al Hussein AFP PHOTO / ADRIAN DENNIS

Yariman Jordan Ali Bin al Hussain yace masoya kwallon kafa a fadin duniya ne suka nuna sun gaji da jagorancin Blatter a matsayin shugaban FIFA, lamarin da har ta kai ake son nada kwamiti domin tsabtace hukumar da sunanta ya baci saboda rashawa karkashin jagorancin Blatter.

Talla

Ali Bin Al Hussian ya yi adawa da Blatter a zaben FIFA da aka gudanar a ranar 29 ga watan Mayu, kuma yanzu yana cikin manyan ‘yan takara da suka hada da shugaban kwallon Turai Michel Platini da ke neman kujerar shugabancin FIFA bayan Blatter ya yi murabus.

Blatter ya ce sai an yi zabe a watan Fabrairun badi sannan zai sauka, amma Yarima Ali na ganin ya dace shugaban ya sauka tun da wuri domin tabbatar da sauyi a FIFA karkashin jagorancin sabon shugaba.

A ganin Yarima sabbin hannu ne ya kamata a nada a kwamitin, musamman a wannan lokacin da ake zargin jami’an hukumar FIFA da karbar cin hanci da ya kai sama da dala miliyan 150.

Kwamitin tabtace FIFA da za a kafa na mutane 10 ne da za a zaba daga hukumomin kwallon kafa daga nahiyoyin duniya, amma Yarima Ali na ganin idan sauyi ake so, to sai an samu sauyin shugabanci kafin a samu biyan bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.