Jimmy Carter na fama da Cutar Kansa
Wallafawa ranar:
Tsohon Shugaban kasar Amurka Jimmy Cater ya fadi da bakinsa cewa yana fama da cutar Kansa, kuma ta bazu a jikinsa.
Jimmy Carter mai shekaru 90 ya kasance Shugaban Amurka na 39. A farkon wannan mako sai da aka yi masa aikin tiyata a wani asibiti.
Carter ya fadi a cikin wata sanarwa cewa zai dauki hutu domin zuwa a diba lafiyarsa a asibitinin Jami’ar Emory a Atlanta.
Shugaban Amurka Barack Obama ya jagoranci sakon fatan samun sauki ga tsohon Shugaban.
Mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden ya tattauna da Carter ta salula inda ya masa fatan samun sauki. Haka ma Hillary Clinton ta yi wa tsohon shugaban addu’a a shafinta na Twitter.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu