Brazil

Shugabar gwamnatin Jamus na ziyarar aiki a Brazil

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel. REUTERS/Antonio Bronic

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a yau alhamis za ta fara ziyarar aiki a kasar Brazil tare da rakiyar wasu ministocinta 6.

Talla

Batun tattalin arziki dai shi ne jigo a lokacin ganawar da za a yi tsakanin Merkel da kuma shugabar Brazil Dilma Roussef wadda a halin yanzu ke fuskantar matsin lamba daga al’umma da kuma abokannin hamayyarta na siyasa dangane da zargin rashawa.

A karshen makon da ya gabata dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zangar nuna kiyayya ga salon mulkin Dilma, wanda suka ce rashawa da kuma karya doka sun dabaibaye shi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.