Isra'ila

Kungiyoyin agaji sun roki Isra’ila kan mamayar Gaza

Wasu Kungiyoyin agaji kimanin 35 a sasan duniya da suka hada da Actionaid da Oxfam sun roki gwamnatin Isra’ila ta kawo karshen kilacewar da ta ke yi wa Zirin Gaza inda al’ummar yankin ke matukar bukatar agajin gaggawa.

Isra'ila ta lalata gidajen Falasdinawa a Gaza
Isra'ila ta lalata gidajen Falasdinawa a Gaza REUTERS/Suhaib Salem
Talla

Tun shekara ta 2006 ne Isra’ila ta killace yankin na Gaza bayan da kungiyar Hamas ta yi nasara a zaben ‘yan majalisar dokokin da aka gudanar.

Kimanin Falasdinawa 2,251 aka kashe a yakin da aka gwabza tsakanin Isra’ila da Hamas a Gaza a bara da suka hada da yara kanana 500. Sojojin Isra’ila 67 aka kashe.

Isra’ila kuma ta lalata gidajen mutanen Gaza da dama a hare haren ta kai wa Hamas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI