Isa ga babban shafi
Guatemala

An cire wa shugaban Guatemala rigar kariya

Masu zanga-zangar adawa da shugaban Guatemala.
Masu zanga-zangar adawa da shugaban Guatemala. Reuters
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau | Garba Aliyu
Minti 1

Majalisar kasar Guatemala ta cire dukkan dokokin da ke kare Shugaban kasar Otto Perez daga fuskantar duk wata tuhuma da ake masa, al’amari da zai bayar da damar a gurfanar da shi gaban kotu game da zarge-zarge da ake masa na kazamin cin hanci da rashawa.

Talla

Wakilan majalisar 132 suka zartas da cire wa shugaban kasar dukkan rigar kariya da ya ke da ita. Kuma shi ne shugaba na farko da aka tube wa rigar kariya a kasar.

Masu adawa da shugaban dai sun barke da murna a harabar ginin majalisar bayan shafe lokaci suna Masu zanga-zanga na neman ganin an tuhumi shugaban da laifukan cin hanci.

Akwai alamun za a tube shi daga mukamin shugaban kasa idan har kotu ta ci gaba da tsare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.