Isa ga babban shafi
Faransa

Alkalan Faransa sun kammala bincike kan mutuwar Arafat

Marigayi Yasser Arafat
Marigayi Yasser Arafat REUTERS/Suhaib Salem/Files
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 2

Alkalan kotu a Faransa, sun kawo karshen binciken da suke gudanarwa a game da zargin yin amfani da guba domin kashe shugaban Falasdinawa Yasser Arafat a shekara ta 2004 

Talla

Alkalan ba su samu wani da hannu ba a mutuwar Arafat kamar yadda wani mai shigar da kara a Kotun na Nanterre dake kusa da birnin Paris na Faransa ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP.

Yasser Arafat dai ya mutu ne a wani Asibitin Soji da ke birnin Paris, a wani yanayi da wasu ke zargin cewa an yi amfani da sinadirin guba na Polonium ne domin kashe shi.

Tun a Ofishinsa dake birnin Ramallah kusa da yamma ga kogin Jordan, Arafat ya fara fama da matsannancin ciwon ciki, kuma daga bisani ya kwanta Asibitin na Paris.

Uwargidansa mai suna Suha ta jajirce cewa an kashe Maigidanta ne ta hanyar bashi guba, to saidai Alkalan sun yi watsi da zargin bayan sun kasa samun kwararan shaidu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.