Isa ga babban shafi
Birtaniya

Faransa da Birtaniya za su karbi ‘Yan gudun hijirar Syria

Dubban 'Yan gudun Hijira ne ke son shiga Jamus
Dubban 'Yan gudun Hijira ne ke son shiga Jamus Reuters
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 1

Shugaban Faransa Francois Hollande ya ce kasarsa za ta karbi ‘Yan gudun hijira kimanin 24,000 cikin shekaru biyu, tare da yin kiran gudanar da babban taro kan matsalar bakin haure da ke ci gaba da kwarara zuwa kasashen Turai.

Talla

Kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana matsalar bakin-haure a matsayin mafi muni tun yakin duniya na biyu.

Birtaniya ma ta amince ta karbi ‘Yan gudun Hijirar Syria kimanin 20,000 a cikin shekaru biyar daga sansaninsu a kasashen Lebanon da Turkiya da Jordan.

Tun da farko Jamus ta bayyana matakin karbar bakin haure 31,400. Kasar ta amince da matakin ne don rage wa kasashen Girka da Italiya da hungary nauyin hidimar bakin hauren.

Shugaba Hollande ya yi gargadi akan daukar matakan da suka dace kan raba bakin hauren tsakanin mambobin kasashen Turai.

Shugaban ya ce nan gaba zai jagoranci taro na musamman kan matsalar bakin haure a Paris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.