Isa ga babban shafi
Falasdinu-MDD

Yau za a daga tutar Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya

Tutar Kasar Falasdinu, da ake shirin daga wa yau a Shalkwar MDD
Tutar Kasar Falasdinu, da ake shirin daga wa yau a Shalkwar MDD Christopher Furlong/Getty Images
Zubin rubutu: Nasiruddeen Mohammed
Minti 2

Watakila yau Alhamis Majalisar Dinkin Duniya ta amince Falasdinawa su daga tutarsu a shalkwatar majalisar, dake birnin New York, matakin da zai karfafa bukatar da suke yi na neman kafa kasar Falasdinu.

Talla

Da misalin karfe uku na rana ne babban zauren mashawartar majalisar, zai jefa kuri’ar amincewa da haka, gabanin ziyarar da shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas zai kai a birnin New York domin halartar taron shekara-shekara na babban zauren majalisar a ranar 30 ga wannan wata na satumba.
Jami’an diflomasiyya suna ganin da alama wannan kudurin na neman daga tutar ta Falasdinu zai sami amincewa wakilan majalisar.
Wakilin Falasdinawa a Majalisar ta Dinkin Duniya Riyad Mansour yace suna da yakinin cewa kasashen duniya suna goyon bayan fafutukar samun kasa mai cin gashin kanta.
Sai dai kuma kasashen Isra’ila da Amurka sun nuna adawa da wannan matakin, inda jakadan kasar ta Yahudu a majalisar Ron Prosor ya nemi Sakatare Janar na Majalisar, Ban Ki-moon da shugaban babban zauren mashawartar majalisar su hana a dauki wannan matakin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.