Isa ga babban shafi
Saudi-Arabia

Al-ummar Musulmi na bikin Eidul Adha

Dubban Musulmi na shagulgulan bikin Eidul Adha ko Eidul Kabir
Dubban Musulmi na shagulgulan bikin Eidul Adha ko Eidul Kabir REUTERS/Muhammad Hamed
Minti 1

Yau Musulmin duniya ke gudanar da bikin Sallar Eid Adha iwanda ake kira babbar Salla a Hausance kuma bikin na zuwa ne kwana kwana guda da kammala hawan Arafa da Alhazai suka yi a Kasar Saudi Arabia.

Talla

Bikin na yau ya kunshi zuwa Massalatai a daidai lokacin da hantsi domin gudanar da Sallar nafila ra’aka biyu da kuma yanka dabbobi musamman raguna ga wadanda Allah Ya hore wa.

Su kuma Alhazai a Saudi Arabia yau zasu fara jifa bayan sun kwana a Musdalifa.

Bikin Eidul Adha wanda ake gudanarwa a duk ranar 10 ga watan Zhul-Hijjah, wato watan karshe na musulunci na cikin manyan bukukuwan da musulmai ke yi a duk shekera.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.