Brazil

Rousseff ta Brazil na fuskantar sabuwar barazana

Dilma Rousseff Shugabar kasar Brazil.
Dilma Rousseff Shugabar kasar Brazil. REUTERS/Ueslei Marcelino

Shugabar Brazil Dilma Rousseff na fuskantar wata sabuwar barazana bayan Kotun Kasar ta nuna rashin gamsuwarta kan yadda gwamnatinta ta kashe kudade ba bisa ka’ida ba, lamarin da ya bai wa ‘yan adawa karfin gwiwa na neman a tsige ta. 

Talla

Kotun wadda ke sa ido kan asusun gwamanatin tarayya ta bayyana rashin gamsuwarta game da yadda gwamantin Rousseff ta gabatar da bayanai kan yadda ta kashe kudeden a cikin shekerar bara harma da yadda gwamantin ta karbi bashi daga bankunan kasar ba bisa ka’ida ba domin cike gibi a kasafin kudinta na shekara, lamarin da Kotun ta bayyana a matsayin karan tsaye ga doka.

A cewar babban Alkalin Kotun, Augusto Nardes, sun ki amince wa da bayanan gwamantin Rousseff ne game da yadda ta kashe kudaden saboda hakan ya saba wa doka.

Tuni dai ofishin Dilma Rousseff ya fitar da wata sanarwa domin kare gwamantinta kan wannan batun, inda sashen shari’a na ofishin ya ce bai kamata a yi watsi da bayanan gwamanatin ba kuma babu dokar da ta ce ayi haka.

Har ila yau gwamanatin Rousseff ta musanta aikata ba dai dai ba.

Tuni dai masharhanta na kasar su ka yi hasashen cewa wannan batun na iya sa a tsige Roussef a matsayin shugabar kasar ta Brazil.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.