Amurka

Amurka ta fitar da rahoto kan addini da ta'addanci

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry.
Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry. Reuters/路透社

Kasar Amurka ta fitar da wani rahoto kan karuwar rashin bai wa jama’a damar gudanar da addininsu a duniya da hare haren ta’addanci a Gabas ta Tsakiya da kuma karuwar kin jinin Yahudawa a Turai.

Talla

Rahotan da Amurka ke fitar wa kowace shekara kan banbancin addini, ya rawaito ma’aikatar harkokin wajen kasar na cewa, duk da kokarin da gwamnatocin kasashen duniya ke yi dan kawo karshen irin wannan cin zarafi, kungiyoyin 'yan ta’adda irin su ISIS na karuwa.

Rahotan ya ce matsalar ba wai ta tsaya kawai a kasahsen da ke adawa da Amurka ba ne irin su Iran da China, amma har da kasashe irin su Saudi Arabia dake hulda da kasar, tare da kasashen da suka ci gaba irin su Faransa da Jamus.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce babu kasar da za ta cimma muradunta muddin ana hana wasu daga cikin al’ummarta gudanar da addinisu, ko kuma bayyana shi.

Rahotan ya ce a cikin watanni 12 da suka gabata, kungiyoyin 'yan ta’adda irin su ISIS a Iraqi da Syria da Book Haram a Najeriya da Chadi sun aikata munanan laifuka wajen dibar rayukan jama’a.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.