MDD-Najeriya

Najeriya, Masar da Ukraine sun samu kujerar Mamba a MDD

Mambobin Majalisar Dinkin Duniya
Mambobin Majalisar Dinkin Duniya REUTERS/Yves Herman

Kasashen Masar, Japan da Senegal, Uruguay da Ukraine sun samu kujera a Ma’aikatar tsaron Majalisar dinkin duniya, toh sai dai Ukraine da ke takun saka da Rasha ta ce wannan kujerar, ba za ta kasance na gajeran lokaci ba kamar yadda wasu kasashen ke yi

Talla

Mambobin zauran Majalisar dinkin duniya 193 ne suka kada Kuri’a da ya baiwa kasashen Nasara kasancewa Mambobi a Majalisar

Masar dai ta samu yawan Kuri’u 179, yayin da Japan ke da Kuri’u 184, sai Senegal mai 187, Ukraine 177 da kuma Uruguay 185.

Wannan kuri’u dai a yanzu zai ba su daman maye gurbin kasashen Chadi, Chile, Jordan, Lithuania da Nigeria a farkon Watan Janairu ba di.

Zauran Majalisar dinkin duniya a bisa al’ada na dauke da Mambobi kasashe 10, kuma a kowacce shekarar a kan zabe sabin Mambobi 5, kana Raguwan 5 kasashen ne masu karfi da kuma ke da kujeran dindidin a Majalisar.

Cikinsu kuwa akwai Amurka, Britaniya, Faransa, China da Rasha, wadanan ke da alhakin yanke hukunci a majalisar.

A cewar Ministan harkokin wajen Ukraine Pavlo Klimkin wannan kujera ba za ta kasance musu na shekaru 2, kamar yadda sauran kasashen ke yi.

Tuni dai masu sharhi suka fara bayyana ra’ayoyinsu dangane da yadda zaman majalisar za ta kasance, lura da rashin jituwa da ke akwai tsakanin Rasha da Ukraine da kuma batun yakin Syria da Musamman Amurka ke soka Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.