Isra'ila-Falasdinawa

Falestinawa 4 ne suka rasa rayukansu a karkashin luguden dakarun Israela

Hoton wasu matasan Falesdinawa agabar yammacin kogin Jodan
Hoton wasu matasan Falesdinawa agabar yammacin kogin Jodan AFP PHOTO / ABBAS MOMANI

A yayinda kasashen duniya ke ci gaba da kiran kawo karshen tashetashen hankulla a yankin Falesdinawa da Isaraela ta mamaye, a jiya jumaa palaestinawa 4 ne suka rasa rayukansu, a cikin wata taho mugama da ta hadasu da dakarun tsaron kasar Israela.

Talla

A yayinda a yankin Naplus dake gabar yammacin kogin Jodan, Falasdinawa maso bore suka bankawa kabarin josef, da yahudawa ke girmamawa wuta

Shugaban kasar Amruka Barak Obama ya bayyana fargabarsa kan ci gaba da kamarin da rikicin ke yi, inda a cikin mako mai zuwa ake sa ran sakataren harakokin wajen kasar Amruka Jon Kerry, zai gana da shugaban Palastinawa Mahmud Abbas, da PM Israela Benjamin Netanyahu domin kawo karshen tashe-tashen hankullan da ke yi a tsakaninsu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.