Isra'ila

Isra’ila za ta yi watsi da bukatar Faransa akan Al Aqsa

Rikicin Falasdinawa da Isra'ila akan Masallacin Al Aqsa
Rikicin Falasdinawa da Isra'ila akan Masallacin Al Aqsa AFP PHOTO/AHMAD GHARABLI

Gwamnatin Isra’ila na shirin bayyana kin amincewarta da bukatar kasar Faransa na tura masu sa ido na kasashen duniya Masallachin Al Aqsa, a wani yunkuri na kawo karshen tashin hankalin da ake samu a kasar.

Talla

Matakin na zuwa ne bayan kwashe sama da makwanni biyu ana dauki ba dadi wanda ya yi sanadiyar kashe Falasdinawa 41 da Yahudawa 8.

Firaminsitan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ki yarda da bukatar Faransa, inda ya aikawa Jakadan kasar da ke Israila takardar gayyata don shaida ma sa matsayin Faransa yau da safe.

Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry ya yi kiran kawo karshen rikici tsakanin Yahudawan Isra’ila da Falasdinawa domin kawo karshen rikici tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.