Amurka -Falesdinu

Amurka ta yi kira zuwa Falesdinu da Isra'ila

John Kerry sakataren harakokin wajen Amurka
John Kerry sakataren harakokin wajen Amurka REUTERS/Andrea Comas

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya jaddada kiransa na kawo karshen rikici tsakanin Jami’an tsaron Isra’ila da Falasdinawa yayin da tsohuwar mai shiga tsakani ta kungiyar Falasdinawa Hanna Ashrawi ta koka kan yadda Jami’an tsaron ke musguna wa Falasdinawa.

Talla

Sakatern harkokin wajen Amurka John Kerry ya bukaci kawo karshen rikicin duk da yake ya nuna goyon bayansa ga ISraila
Tsaro da huldar diflomasiya na tafiya ne kafa da kafa a cewar Kerry wanda da babbar murya y ace suna bukatar gani an kawo karshen wannan rikicin.
Kuma ya na mai kyautata zaton duk wanda ke zaune a Isra’ila da yankin da kasar ke ciki, zai bukaci ya ga haka.

A bangare guda ita kuwa Hanna Ashrawi, tsohuwar mai shiga tsakani ta kungiyar Falasdinawa ta caccaki yanayin yadda Jami’an tsaron Isra’ila ke cin zarafin Falsdinawan.
Ana dai sa ran nanda yan kwanaki masu zuwa, Sakataren harkokin wajen amurka John Kerry zai gana da Benjamin Netanyahu Firai Ministan Israila da kuma Mahmud Abbas shugaban Falasdinu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.