MOLDOVA

An kwace kadarorin Tsohon Firaministan Moldova

Filat  tsohon Firaministan kasar Moldova
Filat tsohon Firaministan kasar Moldova ff.md

Masu gabatar da kara a kasar Moldova sun kwace kadarorin tsohon Firaministan kasar Vlad Filat saboda zargin da ake masa na cin hancin da ya kai Dala biliyan 1 da kuma ya haifar da zanga zanga da ta kai darajar kudin kasar ga faduwar. 

Talla

Tuni kotu ta bada umurnin tsare Tsohon Firaministan na kwanaki 30 yayin da masu bincike ke cigaba da tattara sheidu bayan kama shi a Majalisar kasar.

Rahotanni sun ce a watan Afrilu ne aka gano bankunan kasar sun bada rancen Dala biliyan guda ga wasu mutane da babu wanda ya san ko su waye, sai daga bisani aka gano cewar Firaministan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.