Colombia

Yan Sandan Colombia sun kama mutane dauke da hodar ibilis

Yan sanda a wani shigen bicinke dake kasar Colombia
Yan sanda a wani shigen bicinke dake kasar Colombia AFP

Yan Sanda a kasar Colombia sun kama iyalan wani gida hudu dauke da daurin hodar ibilis 91 da hodar heroin kunse a cikin su.Jami’an yan Sandan sun ce mutanen hudu na kan hanyar su ta zuwa Janhuriyar Dominican ne lokacin da suka fada hannun jami’an tsaro a tashar jiragen saman Cucuta dake iyakar Colombia da Venezuela. 

Talla

Mutanen da suka hada da wata mata mai shekaru 39, da dan ta mai shekaru 21 da wata yarinya mai shekaru 16 da kuma mahaifin ta mai shekaru 67.
Hukumomin kasar sun bayana cewa za su maida hankali tareda gudanar da bicinke a muhiman wurare da suka hada da tashoshin sauka dama tashin jiragen sama kai harma da tashoshin motocin sufuri.
Colombia na daga cikin mayan kasashen duniya da ake noma wanan ganye.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.