Geneva

Cutar tari na kashe dubban mutane a sassan duniya

Likita na bincike kan cutar tari
Likita na bincike kan cutar tari Aurélie Baumel/MSF

Akalla mutane dubu hudu da dari hudu ne cutar tarin fuka ko TB ke kashewa a kowacce rana kamar yadda Hukumar lafiya ta duniya ke cewa a wani rahoto.  

Talla

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce yawan mutanen da ke mutuwa a sanadiyyar kamuwa da cutar ya zo daidai da na cutar HIV duk da kokarin da ake yi wajen bayar da magungunan da kuma hana yaduwar cutar a shekarun bayan-bayan nan.

Hukumar da ke yaki da cutar tarin fuka ta duniya ce ta sanar da hakan a rahotonta na shekara shekara, inda ta ce yawan asarar rayuka da ake samu sanadiyyar tarin ya haura dubu hudu a kowace rana.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI