India-Afrika

Modi ya bukaci a cimma matsaya kan sauyin yanayi

Firaministan India Narendra Modi da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Firaministan India Narendra Modi da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

A jawabin da ya gabatar a gaban shugabannin kasashen Afrika a birnin New Delhi, Firaministan India, Narendra Modi ya bukaci a cimma matsaya mai dore wa dangane da sauyin yanayi a duniya.

Talla

Modi ya bayyana cewa, India da nahiyar Afrika ba sa haifar da dimamar yanayi a duniya kuma ya ce bai kamata laifin mutane kalilan ya shafi jama’a da dama ba.

Kalaman Modi na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin kasashen duniya ke shirin gudanar da taro a birnin Paris na kasar Faransa a watan Disamba domin cimma matsaya kan yadda za a magance matsalar sauyin yanayi a duniya.

Modi ya shaida wa taron wanda ya samu halartar wakilan kasashen Afrika 54 cewa, suna kokari matuka ta hanyar amfani da abinda suka mallaka domin yaki da matsalar ta sauyin yanayi.

Modi ya kara da cewa, suna fatan a cimma matsaya mai dore wa a lokacin da kasashen duniya za su gana a birnin Paris a watan Disamba, kuma matsayar ta yi daidai da ka’idojin da Majalisar Dinkin Duniya ta shimfida kan sauyin yanayi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.